Najeriya: Akwai mafita a sabuwar dokar haraji?
January 17, 2025Gwamnoni Tarayar Najeriyar dai, sun cimma wannan matsaya ne a taron da suka yi da shugaban kwamitin sake fasalin tsarin harajin a Abuja fadar gwamnatin kasar. Bayan kwashe makonni ana takaddama a tsakanin gwamnonin Najeriyar da fadar shugaban kasar musamman wadanda suka fito daga yankin arewacin kasar da suka bijire a kan sabon tsarin rabon harajin na kayayyaki ne, aka cimma wannan sabon tsari a tsakaninsu.
Karin Bayani: Shirin sabuwar dokar haraji a Najeriya
A yanzu sun amince da tsari na a raba kaso 50 cikin 100 na kudin harajin daidai a tsakanin jihohin kasar, sannan kaso 30 ga jihohin da can ne shalkwatar kamfanonin suke maimakon kaso 20 da ake da shi a yanzu. A baya dai kaso 60 cikin 100 ne kwamitin sake fasalin harajin Najeriyar, ya bayar da shawarar a bai wa jihohin da ke da kamfanonin. Akwai ma wani fanni mai mmuhimmanci da suka amince na rabon kudin harajin na VAT, inda za a dogara kan yawan al'umma da kowace jiha ke da shi domin sune ke amfani da kayayyakin da ake sawa harajin.
Gwamnonin sun amince da kaso 20 cikin 100, maimakon kaso 30 cikin 100 da ake amfani da shi a yanzu. Tuni aka fara mayar da martani a kan wannan batu, musamman kungiyoyin rajin kare alumma. Abin da duk ya tayar da wannan takaddama dai shi ne batun bai wa jihohin da shalkwatar kamfanonin suke kaso 60 cikin 100 na harajin kayayyakin na VAT a Najeriyar, wan da gwamnonin da ma al'ummar jihohi da dama suka bayyana cewa wayo ma ya san naki.
Karin Bayani: Zargi 'yan sanda da cin-zarafi a Najeriya
Cima matsayi a tsakanin gwamnonin Najeriyar da kwamitin sake fasalin tsarin harajin kasar na nuna kama hanyar amincewa da kudurorin da ke gaban majalisar dokokin Najeriya, inda can ka takaddamar ce ta haifara da jinkirin aiki a kan kudurorin. Kudurorin dokar harajin dai sun zama wani gwaji ga tafarkin mulkin dimukuradiyya da ya bayar da dama ga 'yan kasa su turje, tare da cewa sun ki kuma a saurare su a kan al'amuran da suka shafi rayuwa.