1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Coronavirus tana ci gaba da ta'adi

Suleiman Babayo ATB
April 20, 2020

Hukumar kula da lafiya ta duniya ta bukaci kara taka tsantsan kan matakan yaki da annobar cutar Coronavirus.

Belgien Bestattungsinstitut Fontaine | Sarg desinfizieren
Hoto: picture-alliance/AP Photo/F. Seco

Hukumar kula da lafiya ta Duniya, WHO, ta yi gargadin cewa da sauran rina a kaba kan yaduwar annobar cutar numbashi ta Coronavirus musamman yayin da aka fara amfanin da sassauta matakan yaki da wannan cuta. Shugaban hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi imanin cutar da yanzu haka ta kama kimanin mutane milyan biyu da rabi kuma daga ciki dubu-166 suka halaka har yanzu ba ta kai ganiyarta ba.

Hukumar ta bukaci kara saka ido da matakai musamman a nahiyar Afirka da ake gani muddun cutar da tsinke kamar abin da aka gani a wasu wurare dubban mutane za su mutu inda tsarin kiwon lafiyar nahiyar ka iya rushewa.

Hukumar kula da laifiyar ta duniya ta nemi yin taka tsatsan doomin kauce wa makacin abin da ya faru shekaru 100 da suka gabata da mutane milyan 100 suka mutu samakaon irin wannan annoba a duniya.