1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIran

Akwai bukatar kai wa masu bore a Iran dauki - Pahlavi

Abdoulaye Mamane Amadou
January 17, 2026

Yariman Iran mai gudun hijira a Amurka, Reza Pahlavi, na son masu kasashe masu bin tafarkin dimokuradiyya su hanzarta daukar mataki kan gwamnatin Iran

Reza Pahlavi daya daga cikin fitattun ’yan adawar Iran
Reza Pahlavi daya daga cikin fitattun ’yan adawar IranHoto: Jonathan Ernst/REUTERS

Dan tsohon jagoran Iran mai gudun hijira yanzu haka a Amurka Reza Pahlavi, ya bayyana wa tashar DW abin da yake tsammani daga gwamnatin  Amurka da Turai wajen tallafa wa masu zanga-zangar Iran.

Pahlavi ya ce ba abin mamaki ba ne ganin yadda kasashen Turai ke jan kafa wajen ayyana rundunar juyin juya halin Iran a matsayin kungiyar ta’addanci, domin a cewarsa, nahiyar na cike da fagabar yadda gwamnatin Iran za ta mayar da martani.

Ya kamata a gaggauta kai dauki wa masu bore

Reza Pahlavi ya kara da cewa ya kamata kasashen da ke fafutikar kare dimokuradiyya da kare 'yanci dan'Adam da daidaiton 'yan kasa ciki har da Amurka da su farga, tare da daukar matakan da suka cancanta ga gwamnatin ta Iran yana mai cewa "Ba mu jiran sai kun dauki mataki kafin mu mu ci gaba da gwagwarmayarmu. Amma ku yi tunanin yadda za mu fi iya kare rayukan bayin Allah marasa laifi da yawa daga mutuwa idan aka dauki mataki tare da taimaka mana tun yanzu". 

Masu zanga-zanga a Iran Hoto: Fatemeh Bahrami/Anadolu Agency/IMAGO

Za a fara zartar da hukuncin kisa kan masu bore a Iran

Reza Pahlavi ya tattauna ne da manema labarai ciki har da tashar dw a Washington DC na kasar Amurka inda yanzu haka yake gudun hijira. Kalaman na zuwa ne a yayin da rahotanni ke cewar an fara dawo da Intanet a Iran, bayan da aka katseta na tsawon lokaci saboda dakile masu bore da zanga-zangar kin jinin gwamnati

Internet ta fara dawowa a Iran 

Kungiyoyin kare hakin bani Adama na kasa da kasa sun bayyana matakin katse intanet din Iran a matsayin wata kafa ta nufin boye ainihin girman danniyar da ake yi wa masu zanga-zanga, wadda ta yi sanadin mutuwar akalla mutane 3,428 tun bayan da aka fara ta karshen watan Disamba, kamar yadda kungiyar Iran Human Rights IHR mai hedkwata a Norway ta bayyana.