'Akwai yiwuwar Trump da Kim Jong Un su gana'
October 18, 2025
Jami'an gwamnatin Trump na tattaunawa a boye kan yiwuwar gudanar da wata ganawa tsakanin Donald Trump da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un yayin ziyarar da ake sa ran shugaban Amurkar zai kai Asiya.
Gidan talabijin na CNN ya ruwaito a ranar Asabar cewa wasu majiyoyi da ke da masaniya game da lamarin ne suka tabbatar mata yiwuwar ganawar.
Trump ya bukaci tattaunawa da Kim Jong Ung
Rahoton ya ce har yanzu jami'an ba su fara shirye-shiryen tafiya ko yin hulda kai tsaye da Pyongyang ba, kuma Koriya ta Arewa ta ki amincewa da kokarin tuntubar da Trump ya yi tun farkon shekarar nan don a gana.
A watan Agusta, Trump ya nuna sha’awar ganawa da shugaban Koriya ta Arewa bayan ya karbi bakoncin Shugaban Koriya ta Kudu, Lee Jae Myung, a Fadar White House a karon farko.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters bai samu tabbacin wannan labarin ba kai tsaye daga hukumomin Amurka, kuma Fadar White House ba ta yi karin bayani ba.