1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Akwai yuyuwar saukar Shugaba Asad na Siriya

August 21, 2012

Duniya na jiron gani ko da gaske Siriya ke yi na tautauna yuyuwar saukar shugaba Bashar

In this photo released by the Syrian official news agency SANA, Syrian President Bashar Assad is shown in an official portrait. (Foto:SANA/AP/dapd) AP PROVIDES ACCESS TO THIS PUBLICLY DISTRIBUTED HANDOUT PHOTO PROVIDED BY SANA TO BE USED FOR EDITORIAL PURPOSES ONLY
Bashar Assad shugaban kasar SiriyaHoto: AP

A wata Ziyarar da ya kai a birnin Mosco na Rasha,mukadashin pramiyan Siriya Qadri Jamil,ya fadawa manema labarai cewar a ci-gaba da neman warware rikicin kasar ta hanyar diplomasiya,gwamnatin zata iya amuncewa da duk wata tautaunawa da 'yan adawa domin kawo karshen rikicin,ciki ya ce har da batun saukar shugaba bashar Al-Assad.
To saidai jami'in ya ce maganar murabus ta shugaban ba zata kasancewa ka'ida ga maganar tautaunawar ba. Wannan sanarwar ta zo ne a daidai lokacain da Amirka ta yi barazanar amfani da karfi idan har Siriya ta yi gigin amfani da makamai masu guba a kan masu tawayen.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Umaru Aliyu