1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alƙawarin afuwa ga fursunonin siyasa a Siriya

June 1, 2011

Jamiyyu da ƙungiyoyin adawar Syriya suna shakkan amincewa da alƙawari afuwar Shugaba Bashar al-Assad

Shugaba Bashar al-AssadHoto: dapd

Shugaba Bashar al-Assad ya yi sanarwar bada afuwa ga fursunonin siyasar ƙasar a wani jawabi da yayi a gidan Talabijin na ƙasa da yammacin jiya. Wannan afuwar ta haɗa da ƙungiyoyin siyasa, a ciki har da jamiyyar 'yanuwa musulmi, wato the Muslim Brotherhood a turance. To sai dai bayan sanarwar afuwar, jami'an tsaro sun cigaba da fatattakar masu boren nuna ƙyamar gwamnati, hakanan kuma, adadin mutanen da suka hallaka sakamakon harin jami'an tsaron ya ƙaru a mahimman biranen da ake zanga-zangar.

Bayan da alummar Syriyar ta shafe tsawon makonni 10 tana nuna adawa da gwamnatin da ke mulki na shekaru goma sha ɗaya yanzu, jamiyyun adawar Syriya sun ce wannan afuwar da shugaba al-Assad ya bayar ba haka nan ba ne, ma'ana da walakin goro a miya, saboda waɗanan fursunoni sun sha wahalar ɗauri da cin zarafin sannan an tashi dare ɗaya ya ce ya bada afuwa, bayan duk turjiyar da masu adawa suka fuskanta a baya. Ammar al-Qurabi wani mai fafutukar kare haƙƙin bil adama ya ce bai ga alamun cewa wani abu zai canza ba:

Masu bore ɗauke da tutar SyriyaHoto: dapd

 " Jami'an tsaro na cin zarafin masu zanga-zanga. Kuma ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba abun daɗa gaba-gaba ya ke yi. kuma babu shakka masu boren zasu cigaba. Idan har aka daƙile duk yunƙurin neman kamanta gaskiyar da alummar ke yi, daga ƙarshe ba za a shawo kan rikicin ta hanyar sulhu ba"

Wannan na ɗaya daga cikin yunƙurin Assad na gudanar da sauye-sauye a tsarin mulkin ƙasar domin biyan buƙatun masu boren, waɗanda suka haɗa da cire dokar ta ɓacin ƙasar wadda ta yi shekaru 48, da kuma bada 'yancin zama ɗan ƙasa ga ƙurdawan da ke gabashin Syriya.

Masu fashin baƙi sun ce cire dokar ta ɓacin da shugaban ya yi a ƙasar, a watan Afrilun da ya gabata bai taɓuka komai ba. A zahiri ma, an cigaba da cafke mutane ana kuma bindge wasu. Dakarun soji, jami'an leƙen asiri da 'yan sanda ba su damu da doka ba kuma basu shayin ta, a saboda haka ne suke ganin cewa haka, ita ma afuwar zata kasance, a matsayin suna, domin kwalliya bazata biya kuɗin sabulu ba.

Wannan sanarwar ta shugaba Assad ta zo daura da wani taron da ƙungoyoyin adawan Syriyan suka ƙaddamar a birnin Antalya da ke Turkiyya, wanda ya sami halartar duk masu adawa da gwamnatin Assad a ƙasashen waje. Kuma wannan alƙawari ta afuwa daga fadar gwamnatin Syriyar a Damascus ta ɗan ja hankalin mahalarta taron.

Ba za'a iya tantance yawan waɗanda suka shiga boren ba, amma ana fargabar adadin su na cigaba da ƙaruwa tun bayan da aka ƙaddamar da boren. Bisa bayanan Fares Braisat, wani ƙwararre a fanin siyasar Larabawa daga Katar, ya ce bai san tsawon lokacin da Assad zai ɗauka kafin ya ɗuki matakin da ya dace ba.

Hoto: AP

"Bana tsammani gwamnatin Syriya ta shawo kan abun da ke faruwa yanzu, illa amfani da ƙarfin sojan da take yi, kuma amfani da ƙarfin soja ba zata yi maganin komai ba."

A wata hira da yayi da wani gidan rediyo a Faransa, Ministan harkokin wajen Faransa Alain Juppé ya ce kamata yayi hukumomi a Syriya su fayyace abun da suke nufi, domin bayar da sanarwar afuwa ba ita kaɗai zata shawo kan matsalolin Syriyan ba.

Sauran ƙasashen ƙetare ma sun daɗe suna neman Majalisar Ɗinkin Duniya, ta yi Allah wadai da mulkin turjiya da danniyar da ke wakana a Syriyan, amma ƙasashe masu ikon ɗarewa kujerar naƙi kamar Rasha da China sun nuna shakka dangane da goyon bayan wannan ƙudiri.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu

Edita: Yahouza Sadissou Madobi