Alƙawarin Merkel kan rikicin kuɗin Girka
August 24, 2012Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi alkawarin taimaka wa Girka warware matsalar karancin kudi da ke addabarta. Bayan da ta gana da firaministan na Girka Antonis Samaras a birnin Berlin, Merkel ta ce za ta yi iya kokarinta domin kasar ta ci gaba da zama cikin rukunin kasashen Turai da ke amfani da Euro. Sai dai ta nemi bakon na ta ya aiwatar da daukacin matakan tsuke bakin aljuihu da aka gindaya wa Kasar ta Girka.
Ko da shi ke dai Samaras ya ce kasarsa a shirye ta ke ta bi ka'idojin na kasashen duniya sau da kafa, amma dai a cewarsa Girka na bukatar karin lokaci kafin ta aiwatar da sauye sauyen tattalin arziki musamma ma matakin nan na ci gaba da tsuke bakin aljuhu. Ko da ita ma Merkel sai da ta bayyana cewar kasar ta Girka na bukatar sararawa kafin ta dora kan inda ta tsaya a yunkurinta na tsumi da tanadi.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi