Al Abadi ya baiyana nassara kan IS a Mosul
July 10, 2017Talla
Wannan dai na zama koma baya mafi girma da IS din ta samu tun bayan da ta ayyana birnin na Mosul a matsayin Daular ta.
Tun da farko a yau Firayim Ministan Irakin Haider al-Abadi ya gana da shugabannin al'ummar Kiristoci marasa rinjaye a Mosul domin tattauna makomar arewacin birnin bayan nasarar kabbabe yan kungiyar IS.
Al Abadi wanda ya isa birnin na Mosul a jiya Lahadi ya kuma gana da kwamandojin sojin inda ya taya su murna kan jaruntakar da suka nuna a yakin.
“Yace muna kan matakin karshe na murkushe Daesh baki daya. An riga an yi musu kawanya kuma an basu zabi su yi saranda ko kuma a kashe su. Wannan shine abin da muka yi. Yawancin yan Daesh a Mosul an hallaka su”.