1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon shugaban kasar Sudan cikin tsaka mai wuya

Zainab Mohammed Abubakar AH
December 6, 2019

A daidai lokacin da tsohon shugaban mulkin kama karya na Sudan Omar Hassan Al-Bashir ke fuskantar yiwuwar yanke masa hukuncin kisa, mata sun samu sassaucin rayuwa a Sudan.

Sudan Khartum Ex-Präsident Umar al-Baschir vor Gericht
Hoto: Reuters/M. N. Abdallah

A labarin da ta wallafa game da Kasar Sudan mai taken "kasar da ta sabunta kanta. Jaridar die Tageszeitung ta ce a daidai lokacin da tsohon shugaban kama karya na Sudan Omar Hassan Al-Bashir ke fuskantar yiwuwar yanke masa hukuncin kisa an soma samun sauyi rayuwa. Kawar da mulkin Al-Bashir a watan Afrilu dai, sannu a hankali yana haifar da sauyi daga tsarin mulki irin na sai-mahadi-ka-ture na shekaru 30 da ya yi. Gwamnatin rikon kwaryar kasar da hukumomin shari'a na sauye-sauye a bangarori dabam-dabam na rayuwar al'ummar kasar. Babban mai shari'a Taj al-Sirr al-Hibr ya nada kwamitin binciken juyin mulkin da aka yi a shekara ta 1989. Al-Bashir ne ya jagoranci sojojin da suka kifar da mulkin Sudan din a wancan lokaci, kuma akwai yiwuwar yanke masa hukuncin kisa a kan batun.

Mata a Sudan a yanzu ba dole ne ba su yi shigar musulunci sabanin lokacin Al Bashir
 A yanzu haka dai al-Bashir mai shekaru 75 da haihuwa yana kurkuku bisa zargin rashawa. Kuma alkalin kasar na fatan hukuncin da za a yanke wa tsohon shugaban zai zama darasi ga sauran masu yunkurin juyin mulki. A yanzu ba dole ba ne matan kasar su yi shigar musulunci, kamar yadda shari'a ta tanadar musu a baya.

Hoto: Reuters/S. Sibeko

Zimbabuwe shekaru biyu bayan faduwar gwamnatin Robert Mugabe har yanzu jama'a ba su ga sauyi ba

 Jaridar Süddeutsche Zeitung ta yi sharhi kan shekaru biyu bayan gwamnatin Mugabe. Jaridar ta ci gaba da cewar a lokacin da aka kifar da gwamnatin Robert Mugabe, al'ummar Zimbabuwe na zaton kasarsu za ta samu ci gaba. Ashe dai wannan hasashen babban kuskure ne. Obert Masaraure shi ne shugaban kungiyar malaman makaranta na kasar wanda ya yi zaman kurkuku sau shida, kana aka saceshi sau biyu. Akwai alamun tabo da munanan raunuka a jikinsa. Ya ce saceshi da aka yi na karshe 'yan kwanaki ne da suka gabata, inda aka yi ta dukansa da gindin bindiga kirar AK 47 a inda yake tsare. Obert kamar sauran 'yan Zimbabuwe da ke fatan sauyi bayan gwamnatin Mugabe, ya tsinci kanshi a cikin wannan halin ne saboda gudanar da zanga-zanga kan halin lalacewar makarantun kasar. Ya shaidar da cewar, a duk lokacin da aka tsareshi, a kan yanke masa albashinsa na wata-wata. A watan Nuwamban shekara ta 2017 Obert na daya daga cikin dubban al'ummar Zimbabuwe da suka yi jerin gwano a kan titunan birnin Harare suna yaga hotunan gwamnatin Mugabe. Sai dai lamari na yau tamkar gara jiya ne. Duba da halin kakani ka yi da kasar ta tsinci kanta a ciki karkashin mulkin Emmerson Mnangagwa.

Barazanar fari a kudancin Afirka ya saka al'ummar yankin cikin mawuyacin hali

Hoto: picture-alliance/AP/T. Mukwazhi

Daga batun wahalhalu na rayuwa saboda bakin mulki sai kuma matsalar fari da ya jefa rayukan miliyoyin al'umma yankin kudancin Afirka da ma dabbobi cikin barazanar yunwa a cewar jaridar Neue Zürcher Zeitung. Jaridar ta ce a kowace rana giwaye na jerin gwano a bakin tabkuna da suka bushe suna neman ruwa. Sama da giwaye 200 suka rasa rayukansu a Zimbabuwe sakamakon matsalar farin. Kasashe da dama da ke nahiyar Afirka dai na cikin matsanancin hali sakamakon sauyin yanayi. Afirka ta fuskanci mafi tsananin fari a wannan shekarar, wanda ba wai dabbobi kawai ba matsalar ta shafa har' ma da mutane. Hukumar tallafin abinci ta MDD ta nunar da cewar akalla mutane miliyan 45 ne ke bukatar agajin abinci cikin watanni shida masu gabatowa a yankin kudancin Afirka, idan aka kwatanta da na shekara ta 2018. Daura da Zimbabuwe, sauran kasashen da matsalar ta fi kamari sun hada da Zambiya da Botswana da Angola da Namibiya da Lesotho da Eswatini da Afirka ta Kudu.