Al-Burhan ya tsallaka rijiya da baya
July 31, 2024Janaral Abdel Fattah al-Burhan babban hafsan sojan Sudan wanda sojojinsa ke gobza yaki da rundunar RSF, cikin gaggawa aka zakuloshi a wani sansanin sojan kasar da ya kai wa ziyara, inda aka kai harin da jirgi marasa matuki a daidai lokacin da yake ziyara cikin sansanin sojan. Hukumomi suka ce akalla mutane biyar suka mutu yayin wani da harin ya fada tsakiyar wani biki da aka shirya gudnarwa a barikin sojan kasar mai nisan kilo mita 100 daga Port Sudan, inda yanzu haka gwamnatin da sojojin Sudan ke jagoranta take da zama. Kafin harin an dai ga shugaba Burhan yana jawabin kai tsaye a gidan talabijin din kasar kafin a katse shirin ba zato. kazancewar yaki ya tilastawa gwamnatin soja kaura daga Khartoum babban birnin kasar izuwa Port Sudan. A yanzu haka mayakan RSF sune ke iko da akasarin birnin na Khartoum da wasu manyan jihohi kamarsu Kordofan da jihar Aljazira ta Tsakiya da kuma Arewacin Darfuh.