1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Al-Burhan ya yi alkawarin zaman lafiya a Sudan

September 26, 2024

Jagoran sojin ya ce sharadin zaman lafiya, shi ne dakarun RSF su fice daga yankuna da suka mamaye a kasar.

Jagoran Sojin Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan
Jagoran Sojin Sudan Janar Abdel Fattah al-BurhanHoto: Craig Ruttle/AP/picture alliance

Jagoran Sojin Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan ya fada wa zauren Majalisar Dinkin Duniya a ranar Alhamis cewa, ya na goyon bayan dawo da zaman lafiya a kasarsa da yaki ya yi wa kaca-kaca.

To amma Janar din ya ce hakan zai faru ne kawai idan aka kawo karshen mamaye yankuna da abokan gabansa na RSF ke yi.

Ya kuma fada cewa wasu kasashe na bai wa mayakan kar-ta-kwana na RSF kudi ta karkashin tebur, sai kuma makamai da karin sojoji, ko da ya ke janar din bai kama sunan wata kasa ba.

Karin bayani:Biden ya bukaci kawo karshen yakin Sudan cikin hanzari

Ko a ranar Alhamis ma an wayi gari da wasu hare-hare da dakarun gwamnatin Sudan suka kai ta sama da manyan bindigogi a birnin Khartoum, a ci gaba da gwabza kazamin fada da dakarun sa-kai na RSF wadanda ke rike da wasu sassa na babban birnin kasar.

Karin bayani:Moussa Faki na neman a kai zuciya nesa a El-Fasher na Sudan

Mazauna birnin suka ce an fara arangama tun wayewar garin Alhamis, a wani farmakin da ke zama na farko da sojojin suka kai cikin watanni domin kwato sassan babban birnin kasar da ke karkashin ikon RSF.