Al-Qaida ta yi watsi tsaigaita wuta a Siriya
February 26, 2016Kungiyar al-Nosra reshen Kungiyar al-Qaida a Siriya ya soki lamirin yarjejeniyar tsagaita wutar yakin Siriyar da ke shirin soma aiki a karfe 12 na daran wannan Jumma'a.A cikin wani sakon murya da tashar talabijin ta Orient News ta wallafa. Shugaban Kungiyar ta Al-Nosra Abu Mohamad al-Golani ya ce wannan rikici na Siriya ba ya kan hanyar kawo karshe, hasalima zai yadu nan da shekaru goma zuwa sauran kasashe mabiya tafarkin Sunna na yankin Gabas ta Tsakiya har a kasar Saudiyya.
A cikin sakon nasa shugaban Kungiyar ta Al-Nosra ya yi kuma suka da kakkausan lafazi ga komitin hadin gwiwar kungiyoyin tawaye da na adawa na kasar ta Siriya na HCN wanda ya ba da sanarwar amincewa da yarjejeniyar tsagaita wutar a wa'adi na makonni biyu.
Haka zalika ya yi kira ga kungiyoyin 'yan tawayen kasar Siriyar da suka kara matsa kaimi wajen kai hare-hare ga sojojin Bashar Al-Assad da sauran 'yan Shi'a a kasashen Iran da labanan.