Al-shaabab ta halaka mutane 11 a Somaliya
August 17, 2020Talla
An shafe tsawon sa'o'i hudu ana gumurzu da wasu kwamdojin kungiyar biyar da suka yi garkuwa da jama'a a hotel din, kafin daga bisani sojan kundunbalan kasar Somaliya su kai ga kwace otel a hannun mayakan na jihadi, ko da yake ma'aikatar tsaron kasar ba ta kai ga yin wani karin haske kan yadda aka kubutar da wasu tarin jama'a da aka yi garkuwa da su ba.
Wani kamfanin mai zaman kansa da ke aikin agaji a kasar, ya tabbatar da samun akalla mutun 28 da suka jikkata, a yayin da kuma wasu rahotanni ke cewa daukacin maharan biyar sun rigamu gidan gaskiya.