Al shabaab ta halaka mutane
February 4, 2019Talla
Rahotannin da ke fitowa daga Mogadishu babban birnin kasar Somaliya, na cewa kungiyar al Shabaab ta halaka akalla mutum 11 a wani harin bom da ta kaddamar kusa da wata cibiyar hada-hada da ke a birnin.
'Yan sanda sun tabbatar da harin wanda ya shafi wasu cibiyoyin da suka hada da bankuna da shuganan sayar da hajoji.
Harin dai an kai shi cikin wata motar da aka shake ta da boma-bomai, wadda aka tsayar da ita a harabar cibiyar.
Akwai kuma wasu mutum 15 da suka jikkata a lamarin a cewar hukumomin tsaro a Somaliyar.
Al-Shabaab dai na ikirarin jihadin neman kafa gwamnati ne a kasar wacce ta saba wa tsarin kasashen yamma.