1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al-Shabaab ta kashe rayuka a Mogadishu

August 20, 2022

Rahotanni daga Somaliya na cewa wasu manyan fashe-fashe da suka auku da yammacin Juma'a, sun halaka rayukan fararen hula a wani gidan saukar baki da ke birnin Mogadishu.

Somalia - militante Übernahme von Hotel in Mogadischu
Hoto: REUTERS

Mayakan tarzoma na kungiyar al-Shabaab da ke gwagwarmaya da makamai a yankin kuryar Afirka, sun kai hari a wani babban Otel da ke Mogadishu babban birnin kasar Somaliya, inda rahotanni ke cewa ya salwantar akalla mutum 12.

'Yan sanda sun ce da fari maharan na al-Shabaab sun tayar da wasu nakiyoyi ne kafin su kai ga shiga Otel din wanda jami'an gwamnati da 'yan jarida da ma 'yan kasuwa ke zuwa.

Jami'an tsaron sun ce sun kubutar da wasu baki akalla 60 da yammacin jiya Juma'a lokacin da aka kai harin.

Sai dai har yanzu, akwai fargabar cewa mutane da dama na cikin ginin Otel din.