Al-Shabaab ta musanta kashe 'ya'yanta
November 12, 2017Talla
Sheikh Abdiasisi Abu Mus'ab da ke zaman wani kusa a kungiyar ta al-Shabaab ne ya musanta ikirarin, inda kuma ya zargi gwamantin Somaliya da zuki-ta-malle kan harin da aka ce an kaddamar kan kungiyar a babbar tungarsu da ke Jilib a Kudu da Mogadishu babban birnin kasar. A wannan Asbara din ne gwamnatin kasar Somaliyar ta sanar da nasarar halaka mayakan na al-shabaab 81. Ita ma Amirka a ranar Alhamis ta sanar da kai wani farmaki kan kungiyar. Cacar baka kan nasarorin kaddamar da hare-hare tsakanin gwamnatin Somaliya da bangaren na al-Shabaab dai ba sabon abu bane, inda galibi ake gaza iya tantance hakikanin gaskiyar lamarin.