al-Shabaab ta yi kashe-kashe a Somaliya
November 28, 2016![Somalia Autobombenanschlag in Mogadischu](https://static.dw.com/image/36535130_800.webp)
Talla
Wannan artabun ya faru ne biyo bayan martanin kare kai na wani matakin tilasta biyan haraji da 'yan tada kayar bayan suka kakaba wa mazauna yankin. Hukumomin tsaro a Somaliya sun tabbatar da kashe 'yan bindigan 26, tare da wasu fararen hula da manoma da suka fafata da mayakan na al-Shabaab.
kawo yanzu dai babu martani daga bangaren mayakan al-Shabaab kan wannan sabon hari, amma a baya dai sun sha daukar alhakkin munanan hare-hare da ke sanadiyar rayuka da dama, tun bayan da suka lashi takobin kalubalantar gwamnatin Somaliya. Tuni dai aka dauki matakan kara jibge jami'an tsaro a kauyen Dumaaye don kare mazauna yankin.