Mayakan al-Shabab sun kashe sojojin Kenya
July 29, 2026
Talla
‘Yan sanda sun na ci gaba da bin diddigin maharan, bayan da wata tawagar karin jami’ai da aka tura yankin ta gamu da wani bam da aka binne a hanya, wanda ya lalata wata motar sulke. Sai dai ba a samu asarar rai ba.
A watan Janairu, ‘yan sanda sun ce mayakan sun kashe wani shugaban kauye da kuma wani malami a gundumar Garissa da ke makwabtaka da yankin.
Hare-haren al-Shabab a yankin na yawan kai wa sojoji da fararen hula hari don cimma burin kifar da gwamnatin Somalia, tare da kafa nata mulki bisa tsauraran dokokin shari’ar Musulunci.