SiyasaSiriya
Ahmed al-Sharaa zai je Majalisar Dinkin Duniya
August 25, 2025
Talla
Ahmed al-Sharaa wanda ya kwace iko a hannun gwamnatin hambararren shugaban kama-karya Bashar al-Assad a watan Disambar bara, zai kasance shugaban kasar Siriya na farko da zai yi jawabi ga Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniyar. Wani jami'in ma'aikatar harkokin wajen Siriyan da ya nemi a sakaye sunansa saboda ba shi da izinin yin magana da 'yan jarida ne, ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.