Al-sisi ya gamu da fushin Misirawa
May 28, 2014Mahukunta a kasar Masar sun kara wa'adin kwanakin gudanar da zabe, inda a yau Laraba rana ta uku za'a ci gaba da kada kuri'a, sabanin kwanaki biyu da aka tsara. Wannan dai ya biyo bayan karancin fitowar masu kada kuri'a, abinda koma ya zama wani mummunan koma baya da rashin goyon bayan jama'a, ga jagoran juyin mulki Abdel Fattah Al-sisi, wanda ke hanyar shiga fadar mulki. Masu sa'ido suka ce rashin fitowar jama'a ya nuna a zahiri, bawai 'yan kishin Islama da ke adawa kawai ne ba, amma sauran jama'ar Masar basa yin farin cikin kasancewarsa shugabansa, wanda zai iya warware matsalar kasar. Shugaban hukumar zaben yace kimanin kashi 35 cikin dari na 'yan kasar da suka isa kada kuri'a ne suka fito kada kuri'a, abinda ya yi kasa matuka, idan an kwatanta da zaben Mursi wanda aka hambare, a lokacin zaben Mursi ya samu fitowar jama'a kusan kashi 52 cikin dari.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Editor: Umaru Aliyu