Al'adar shan kofi ko gahawa ta isa Najeriya
April 13, 2016'Yar kasuwar daga kasar Kenyar mai suna Nasra Ali ta yanke hukuncin haka ne don ganin Najeriya ta mai da hankali kan noma don rage dogaro da man fetur.
A baya dai, Najeriya ta kasance a cikin masu fidda ganyen kofi ko gahawaizuwa sauran kasacen duniya. To amma tun lokacin da kasar ta gano bakin zinare wato man fetur a shekarun 1960, sauran masana'antun kasar ke fuskantar koma baya. Wannan dalilin ya sa Nasra Ali ta yi nazarin bunkasa harkar kofi a fadin kasar. A yanzu dai masu noman ganyen kofi a Najeriya na dab da cin gajiyar samun horo na musamman kan yadda za su samar da ingantaccen kofi.
"Muna bukatar samun nagartaccen ganyen gahawa, sannan akwai bukatar a koya wa masu noman kofi ko gahawa dabaru ta yadda za su sami saukin aikin. Bai dace ka ci gaba da shanya ganyen a waje ba, kana ba ka barin shi ya girma sosai. Akwai bukatar manomi ya zama mai kuzari a ko wane lokaci."
A yanzu dai, Nasra Ali ta gano cewa kudancin Najeriya na da yanayin noman ganyen kofi. To sai dai 'yar kasuwar daga Kenya na da niyar kafa rassan huldar kasuwanci a jihar Taraba da ke arewacin Najeriyan don kulla alaka da kananan manoma.
Tururuwa don shan kofi a Legas
A wani sanannen shagon sai da kofi a babbar cibiyar kasuwancin Najeriya wato Legas, mutane da dama ke halarta don samun dandanon kofi dabam-dabam daga kasashen Afirka. Sai dai duk da tarin kwastamomin da ke turuwa zuwa shan kofi a shagon, amma ba 'yan Najeriya ne ke diban garabasar ba. Nasra Ali ta ce akwai bukatar samun karin masu sarrafa kofi da zai wadaci al'ummar kasar mai yawan mutane kimanin miliyan 180.
"A yanzu haka dai, muna shigo da kofi daga sauran kasashe makwabta, amma dai muna alfahari da cewa mu ne na farko da ke samar da kofin a fadin kasar. Muna da injunan sarrafa kofi sannan muna kokarin kulla yarjejeniya da wasu otel-otel don samar masu da kofi."
A yanzu Nasra Ali, na son fadada niyyarta na ganin ta ja hankalin manoma da ma sauran kamfanoni wajen bunkasa sana'ar noman ganyen gahawa ko kofi a fadin kasar.