Shugaban Amirka Joe Biden na ziyara irinta ta farko a Gabas ta Tsakiya, wacca ya farota daga Isra'ila kafin ya zarce zuwa yankunan Falasdinawa da kuma kasar Saudiyya.
Talla
Ziyarar da tun kafin farata aka bayyana cewa babban jigonta shi ne inganta tsaron Isra'ila da kawayen Amirka da ke yankin, tare da yunkurin zawarcin karin kasashen yankin domin su kulla hulda da Isra'ila da kara mayar da Iran saniyar ware. Daga bisani kuma za a yi batun farfado da shirin zaman lafiya tsakanin Falasdinawa da Isra'ila. Gwamnatin rikon kwaryar Isra'ila dai ta zuba ruwa a kasa ta sha domin murnar wannan ziyarar da take ganin za ta ba ta damar cimma nasarorin da za ta iya yin gangamin yakin neman zabe da su.
Rikicin Gabas Ta Tsakiya cikin hotuna
Ruwan rokoki a Tel Aviv, rusau a Gaza - Rikici tsakanin Israila da Falasdinawa na kara yin kamari a 'yan kwanakin nan. Sai dai kamar kullum farar hula daga bangarorin biyu sune ke shan wuya.
Hoto: Mahmud Hams/AFP/Getty Images
Israila na kai harin ramuwar gayya
Barnar ba ta kare ba. Jiragen yakin Israila na luguden bama bamai a kudancin Gaza inda ta ke kai hari kan kungiyar Falasdinawa ta Hamas.
Hoto: Said Khatib/AFP/Getty Images
Isra'ila ta kira dakarun wucin gadi
Rundunar sojojin Israila na yin gangamin dakaru da tankokin yaki a kan iyaka da zirin Gaza lamarin da ke tunato da abin da ya wakana a yakin 2008 da 2009 da kuma 2014.
Hoto: Amir Cohen/REUTERS
Hudowar rana
Hayaki ya turnuke sararin samaniya a wannan Laraba a Khan Younis a yankin zirin Gaza. Tun a farkon mako rikici tsakanin Israila da Falasdinawa ya barke a bainar jama'a.
Hoto: Youssef Massoud/AFP/Getty Images
Neman tsira da rayuwa
A birnin Gaza, wadannan falasdinawan sun guje wa farmakin Israila a ranar Talata. Akalla ‘yan Israila takwas suka rasu yayin da ma’aikatar lafiya ta Falasdinawa ta ruwaito cewa akalla mutane 109 suka rasu run daga ranar Litinin.
Hoto: Mahmud Hams/AFP/Getty Images
Rusau a birnin Gaza
Israila ta ce ta kai hari kan gidaje kamar wannan a birnin Gaza, wanda ke dauke da ofisoshi na ‘yan kungiyoyin ‘yan bindiga ko kuma inda shugabannin tsagerun ‘yan Hamas ke zaune.
Hoto: Suhaib Salem/REUTERS
Harin rokoki a Tel Aviv
Kungiyar Hamas da ke mulki a zirin Gaza ta harba rokoki cikin Tel Aviv a daren ranar Laraba. Na’urorin kakkabo makamai masu linzami na Isrila suna bada kariya ga birnin tare da lalatawa ko kuma sake tankada makaman masu linzami zuwa sama yadda ba za su yi wani lahani mai yawa ba.
Hoto: AnAs Baba/AFP/Getty Images
Jira cikin kaguwa
Sai dai kuma na’urar kakkabo makaman masu linzami da ake kira “Garkuwar karfe“ ba ta samar da kariya dari bisa dari. Idan aka busa sarewa dukkan ‘yan Israila sai su bazama neman mafaka cikin gaggawa. Ko da kuwa da karfe uku ne na dare kamar wannan safiyar a nan.
Hoto: Gideon Marcowicz/AFP/Getty Images
Har yanzu akwai hadari
Ko da za a kakkabo rokokin Falasdinawa, baraguzai da ke fadowa suna da hadari. An lalata wani gida a wannan yankin Yahudawa da ke arewa da babban firin jirgin saman Israila. A cewar sojojin Israila Falasdinawa sun harba rokoki fiye da 1000 tun daga ranar Litinin.
Hoto: Gil Cohen-Magen/AFP/Getty Images
Hannu a Ka
Duk wanda bai iya samun mafaka akan lokaci ba, kan yi kokari bakin iyawarsa yadda zai tsira kamar wadannan mutanen a yankin Ashkelon da ke tazarar kilomita 10 daga arewacin zirin Gaza.
Hoto: Jack Guez/AFP/Getty Images
Duwatsu da gwangwanayen hayaki mai sa hawaye
A ‘yan kwanakin baya bayan nan ana ta samun gagarumar zanga zanga tsakanin Falasdinawa da jami’an tsaron Israila a birane da dama, kamar nan birnin Hebron a yankin da Isriila ta mamaye a gabar yamma. Masu zanga zanga na ta jifa da duwatsu da sauran abubuwa.
Hoto: Hazem Bader/AFP/Getty Images
Hotuna 101 | 10
Yarjejeniyar Qudus da aka shirya za a rattaba hannu a kanta tsakanin firaministan Isra'ila da shugaban Amirka yayin ziyarar dai, za ta kara bai wa Isra'ilan lamunin tsaro daga duk wata barazanar ketare ko hare-haren makiya da kuma ake sa ran fadadata ta hade da tsaron kawayen Amirka a yankin. Duk da jaddada goyan bayansa ga kafuwar kasar Falasdinu da Biden ya yi, hukuma Falasdinawan ta bakin kakainta na ganin hakan tamkar raina musu hankali ne kawai.