1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Alakata da Trump ba ta girgiza ba - Merz

April 29, 2026

Shugaban Gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya fadi haka ne bayan da aka jiyo shi ya na cewa Iran ta kunyata Amurka.

Shugaban Gwamnatin Jamus  Friedrich Merz ya fadi haka ne bayan da aka jiyo shi ya na cewa Iran ta kunyata Amurka
Shugaban Gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya fadi haka ne bayan da aka jiyo shi ya na cewa Iran ta kunyata AmurkaHoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Shugaban Gwamnatin Jamus Friedrich Merz, ya bayyana cewa har yanzu dangantakarsa da shugaban Amurka, Donald Trump tana da kyau duk da saɓanin da ya shiga tsakaninsu kan yaƙin Iran.

Tarayyar Turai ta ki goyon baya a yakin Amurka da Isra'ila a Iran

Sai dai Merz ya sake jaddada damuwarsa kan tasirin tattalin arzikin da rikicin ke haifarwa.

Wannan saɓani ya nuna bambancin ra'ayi tsakanin gwamnatin Trump da ƙawayenta na Turai a ƙungiyar NATO kan Iran da sauran batutuwa, ciki har da rikicin Ukraine.

Merz ya shaida wa manema labarai cewa, a ganinsa, dangantakata ta kashin kai da shugaban Amurka har yanzu tana da kyau.

Duniya na yi wa Trump jaje bayan ya tsallake rijiya da baya

Merz ya kuma bayyana cewa Washington da Berlin na ci gaba da tattaunawa da juna.