Haske na farko na samun matsaya a taron kolin EU
July 20, 2020Shugaban majalisar zartaswar kungiyar tarayyar Turai, Charles Michel ya ce ya gabatar da sabuwar shawara dangane da tallafgin ceto tattalin arzikin Turai da ya fuskanci karaya sakamakon annobar Corona. Michel ya yi fatan za a samu tudun dafawa a taron kolin da aka shiga kwana na hudu ana yi a birnin Brussels. Ya ce dama in aski ya kai gaban goshi ya fi zafi amma ya ce yan ad yakinin za a kai gaci.
Da farko jami'an diplomasiyya sun ce kasashe 27 na kungiyar sun amince da yawan kudaden da suka kai Euro miliyan dubu 390 maimakon miliyan dubu 500 na cetom tattalin arzikin Turai.
Shi ma da yake magana gabanin shiga zagaye na gaba a taron Firaministan Italiya Giuseppe Conte ya ce dole a yi takatsantsan, amma duk da haka zan iya cewa ina da kyakkyawan fata."
Ita ma shugabar gwamnmatin Jamus Jamus Angela Merkel ta yi kyakkyawan fata za a cimma yarjejeniya a karshen taron kolin.