Alamun sasanta rikicin jam'iyyar PDP a Najeriya
March 26, 2026
Wannan karon farko da aka hango alamu na shawo kan rikicin cikin gida na jamiyyar ta PDP da ya faro trun karshen shekara ta 2023 a lokacin da ministan Abuja Nyesom Wike ya jagoranci wasu gwamnoni suka yiwa jamiyyar zagon kasa, lamarin da ya ci gaba da yi mata lahani.
Akwai masu ganin hasken tattaunawa
Shugaban jamiyyar ta PDP Kabiru Tanimu Turaki ya ce a yanzu sun kusa gano bakin zaren bisa ga shawarar da kotun da aka kai su kara ta ba su, kuma suna tattaunawa da bangaren Nyesom Wike da suka ja daga da su. Sanata Umar Ibrahim Tsauri dan kwamitin amintattu ne na jamiyyar PDP ya bayyana sunau kwarin guiwana sake hadewa a karkashin inuwar lemar PDP.
‘Yan banagaren da ke samun goyon bayan minsitan Abuja Nyesom Wike a jamiyyar sun yi gum a kan wannan sabon yunkuri na sulhuntawa. Daya bayan daya dai gwamnonin jam'iyyar ta PDP sun gama darewa inda suka chanza sheka zuwa jamiyyar APC mai mulki, inda a yanzu sauran gwamononi biyu suka rage mata, daya daga cikin Bala Mohammed gwamnan Bauchi ya ce sun dade da gano makrkashiyar da ake yi masu.
HAr yanzu da sauran aiki
Duk da murna na fara hangen mafita daga matsala ta rikicin cikin gida da ya tabaibaye jamiyyar ta PDP akwai tsoron abin da ka iya faruwa da wannan kokari, domin jam'iyyun siyasun Najeriya a yanzu shirye-shirye suke na tsara dubarun yadda zasu fuskanci babban zaben da za a yi a Najeriya a watan Janairun shekara mai zuwa ba wai batun sasanta rikicin cikin jamiyya ba. Wannan na jefa tsoron abinda ka iya faruwa. Farfesa Abubakar Umar Kari masanin kimiyyar siyasa da ke jami'ar Abuja ya ce akwai bukatar yin taka tsantsan.
Jam'iyyar PDP ta dakatar da taron kwamitin zartaswarta domin sa ran sakamakon wannan sulhun da suke yi a yanzu. Sake farfado da jam'iyyar PDP zai kara daidaita dimukurdiyyar Najeriya da ke fuskantar kalubale saboda jam'iyya daya da ke mulki wacce a yanzu ke da karfin gaske a fagen siyasar kasar.