1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'amuran da suka ja hankalin Jaridun Jamus a Afirka

Zainab Mohammed Abubakar M. Ahiwa
June 17, 2022

Batun zubar da jini a Burkina Faso da aika ‘yan ci-rani daga Birtaniya zuwa Ruwanda da ma halin karanacin abinci da nahiyar ta shiga sun dauki hankali a jaridun Jamus.

Burkina Faso Militärpatrouille
Hoto: OLYMPIA DE MAISMONT/AFP

Jaridar die tageszeitung wadda ta buga labari mai taken "Zubar da jini a Burkina Faso a matsayin gwajin karfin ikon sojoji."

Kimanin mutane 200 ne ake fargabar sun mutu a wani samame da aka kai cikin dare a garin na gabashin kasar. Sojojin da ke mulki tun watan Janairu, sun kasa kawo karshen tashin hankalin. Har yanzu dai akwai jita-jita game da abin da ya faru a karshen mako a garin Seytenga da ke arewa maso gabashin Burkina Faso. Amma tun daga ranar Lahadi, gidan rediyon Omega ya ruwaito yadda dubban mutane ke kaurace wa karamin garin mai yawan  al'umma dubu 32 zuwa babban birnin lardin Dori, mai nisan kilomita 40 cikin firgici da zullumi. Mahukuntan Dori sun sanar da yin rajistar 'yan gudun hijira 3,173 a ranar Lahadi, kuma galibinsu kananan yara.

Wani faifan bidiyo da aka yayata a shafukan sada zumunta ya nuna Seytenga a daren Lahadin da aka kai harin, inda aka kone gidaje. Wata 'yar jarida a kasar, Aissatou Cissé ta bayyana cewar, tsawon kwanaki uku maharan suka yi suna shiga gida-gida suna kashe mutane, kuma akasarin wadanda aka kashen maza ne.

Akwai sabanin bayanai dangane da yawan mutanen da aka kashe, sai dai ana ganin wannan shi ne hari mafi muni da aka kai kan fararen hula a Burkina Faso tun bayan barkewar rikicin masu tsananin kishin addini a shekarar 2016.

"Gwamnatin Birtaniya ta so ta kori 'yan gudun hijira da dama zuwa Ruwanda, amma jirgin farko ya kusa zama babu kowa". Wannan shi ne taken sharhin da jaridar Süddeutsche Zeitung ta wallafa cikin makon game da shirin tasa keyar 'yan cirani da ke neman mafaka a Birtaniya zuwa Ruwanda bisa yarjejeniyar kudi da kasashen biyu suka cimma.

Hoto: Ben Stansall/AFP

A yammacin ranar Talata ne jirgin farko ya kamata ya tashi daga birnin Landan zuwa kasar Ruwanda dauke da 'yan gudun hijira 37, wadanda za a yanke hukuncin neman mafakarsu a kasar ta gabashin Afirka, ba Birtaniya ba. Kimanin Euro miliyan 140 ne gwamnatin Boris Johnson ke shirin biyan Ruwanda a matsayin domin karbar 'yan ci-ranin kuma akwai yiwuwar karin wasu kudade, ya danganta da adadin ‘yan gudun hijirar da aka aike zuwa Kigali. Yawansu zai iya kai mutum 300 a shekara.

A cikin jirgin farko, an tsara jigilar fasinja goma sha daya. Sauran mutane 26 da ake shirin kora na iya kalubalantar korar ta su a gaban kotu, kuma a wasu lokutan gwamnatin kasar ta janye hukuncin. Daga cikin sauran mutane 11 da ya dace a yi jigilar su zuwa gabashin Afirka a ranar Talatar dai, akwai 'yan Iran hudu da Iraki biyu, da 'yan Albaniya biyu da kuma dan Siriya guda. Kafin kotun Turai da kungiyoyin kare hakkin dan Adam su shiga lamarin gadan gadan.

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung labari ta buga game da halin da ake ciki na matsalar karancin abinci a kasashen Afirka, sanadiyyar yakin Ukraine. A labarin nata mai taken "Fahimtar Afirka game da Putin" jaridar ta ce gamayyar Afirka ta damu ne da bukatun kanta amma ba halin da Ukraine ke ciki ba.

Hoto: DW

Tan miliyan 20 na hatsi na makale a tashar jiragen ruwa na Odessa na tekun Bahar Maliya. A halin da ake ciki kuma, dubban kilomita ta kudanci a nahiyar Afirka, yunwa na kara tsananta. Afirkar dai na dogaro da fiye da kashi 40 na alkama daga Rasha da Ukraine. Gaskiya ne cewa Afirka gaba daya tana da isasshen kasa mai albarka don wadatar da jama'a. Amma saboda dalilai da dama, kama daga rashin wadatattun ababen more rayuwa zuwa wadatar amfanin gona da fari zuwa rikice-rikice, kasasashe da yawa sun dogara ne kan shigo da abinci daga ketare. Afirkar dai bata ganin laifin Rasha dangane da kayan abinci da ke makale a tashar jiragen ruwan na Odessa.

Kamar yadda ya bayyana a ganawar Putin shugaban kungiyar Tarayyar Afirka, Macky Sall lokacin ziyararsa, har yanzu babu abun da ya taba kyakkyawar dangantakar kasashen Afirka da Rasha. Sai dai Amirka da Turai na zargin Rasha da karancin abinci da nahiyar Afirkar ke fuskanta.