SiyasaAfirka
Ouattara zai tsaya takara a zaben Oktoba
August 7, 2020Talla
Shugaban ya bayyana haka ne a cikin wani jawabi da ya yi na minitoci 25 a jajibirin bikin zagayowar cikar shekaru 60 da kasar ta samu 'yancin kai.
Ya ce ''Na yanke shawarar amsa kiraye-kirayen da 'yan kasata ke yi mani na tsayawa takara, don haka zan yi takara a zaben 31 ga watan Oktoba.''
Tun farko Alassane Ouattara ya yi furcin cewar ba zai tsaya takarar ba, to amma bayan mutuwar firaministan kasar Amadou Gon Coulibaly ya canza ra'ayi, sai dai 'yan adawa sun ce ba za ta sabu ba.