1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Albashi ya gagari wasu gwamnoni a Najeriya

April 18, 2017

Akalla jihohin Tarrayar Najeriya goma sha tara a halin yanzu ke fuskantar matsaloli na kasa biyan albashin ma’aikata a cikinsu.

Muhammadu Buhari speaks during an interview with Reuters at a private residence in Lagos, Nigeria
Hoto: Reuters/A.Akinleye

Sama da Dalar Amurka miliyan dubu uku ne dai ake jin sun isa ga aljihun jihohin kasar 36 da nufin kaiwa ga kare matsalar biya na albashi da ma tafi da harkokin mulki na jihohin.To sai dai kuma daga dukkan alamu har ya zuwa yanzu suna cikin matsala don kuwa wasu jihohi sun gagara sauke nauyin da ke kansu na biya ma'aikata hakkokinsu.

Kungiyar ma'aikatan kasar ta ce jihohi goma sha tara ne ke gwagwagwakan batun na biyan albashin duk da tallafi daga hannun gwamnatin tarrayar kasar.

Babban buri na tallafin a idanu na gwamnatin dai na zaman iya kaiwa ga biyan albashin sannan da rage na da da ma a cikin dimbin bashi dama aiyyukan raya kasa.

Hoto: dapd

Sabuwar matsalar da ke neman harzuka ma'aikatan kasar da jihohin dai na nuna irin jan aikin da ke gaban kasar da ke fatan rage wahalar 'yan aikin amma kuma ke neman karewa a cikin sabon rikici.

Comrade Ayuba Wabba dai shi ne shugaban kungiyar kwadagon kasar ta NLC wanda ya ce adalci na zaman na wajibi da nufin kaucewar rikici a tsakani na jihohin da ma'aikatan da ke kallon wakaci ka tashi.

Sabuwar matsalar da ta tabo jihohi cikin Arewacin kasar da ma Kudu dai, daga dukkan alamu na iya mayar da hannun agogo zuwa can baya a kokari na farfado da harkoki cikin jihohin da tuni suka dau hanyar 'yar rikici da masu kodagon.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani