Labarin Wasanni: Alcaraz ya lallasa Djokovic
February 2, 2026
Za mu dauko shirin da wasan Tennis na Australiya da ya kawo karshe, inda Carlos Alcaraz ya samu nasara a bangaren maza tare da doka Novak Djokovic. Alcaraz mai shekaru 22 a duniya dan kasar Spain, ya zama mafi karancin shekaru da ya samu irin wannan nasara. Ita dai wannan nasara ta nuna yadda tasirin Novak Djokovic mai shekaru 38 da haihuwa dan kasar Sabiya, ya fara raguwa a fagen wasan na tennis a duniya. A bangaren mata kuma, Elena Rybakina ta doke Aryna Sabalenka a wasan karshe da 6–4 da 4–6 da 6–4.
Kungiyar Werder Bremen da take matsayi na hudu daga kasan Teburin Bundesliga na Jamus kuwa, ta sallami mai horas da 'yan wasan kungiyar Horst Steffen bayan watanni bakwai kacal saboda yadda aka kwashe wasanni 10 a jere ana samun galaba kan kungiyar. Tuni aka nada Raphael Duarte da Christian Gross domin su maye gurbin mai horas da 'yan wasa da na wucin gadi, har zuwa lokacin da za a nada sabon mai horas da 'yan wasan. A sauran wasannin na Bundesliga da aka kara kuwa, an tashi kamar haka:
Cologne 1, Wolfsburg 0
RB Leipzig 1, Mainz 2
Bremen 1, Monchengladbach 1
Augsburg 2, St. Pauli 1
Hoffenheim 3, Union Berlin 1
Hamburger SV 2, Bayern 2
Eintracht Frankfurt 3, Bayer Leverkusen 1
A wasannin La Liga da aka kara a Spain, Barcelona ta bi Elche har gida ta ragargazata da 3 da 1. Ita kuwa Real Madrid da kyar da jibin-goshi bayan karin mintoci 10 a karshen wasa da kuma bugun da kai sai mai tsaron gida har da katin kora, kafin ta iya cinye Rayo Vallecano da 2 da 1. Sannan Betis da Valencia sun tashi 2 da 1.
Yanzu haka a jerin teburin na La Liga:
Barcelona maki 55
Real Madrid maki 54
Atletico Madrid maki 45
Villarreal maki 42
Espanyol maki 34
A wasan Premier League da aka kara a Ingila, kungiyar Arsenal ta bi Leeds har gida ta doke ta da 4 da nema. Haka Chelsea ta doke West Ham da 3 da 2, yayin da Liverpool ta kassara Newcastle 4 da 1. Sannan Manchester United ta lallasa FC Fulham 3 da 2, kana Nottingham da Crystal Palace sun tashi 1 da 1.