1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Minista ya bar aiki saboda alfarbar rigakafin corona

Abdul-raheem Hassan
February 20, 2021

Ministan lafiya a kasar Ajantina Gonzalez Garcia, ya ajiye aiki bayan da shugaban kasar Alberto Fernandez ya umarce shi da yin haka bayan yi wa abokansa alfarmar allurar rigakafin corona.

Argentinien Gines Gonzalez Garcia
Hoto: Juan Mabromata/AFP/Getty Images

Rikicin ya yi kamari ne bayan da wani dan jarida mai shekaru 71 ya sanar a rediyo cewa ya samu allurar a ofishin ministan gabannin a fara yi wa al'ummar kasa saboda dadadden abotar da ke tsakaninsu.

Wasu kafafen yada labarun Ajantina sun ruwaito 'yan uwa da abokan ma'aikatan gwamnati, sun samu allurar a ma'aikatar lafiya gabannin a fara yin allurar a hukumance a ranar Laraba mai zuwa.