1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar kyamar sake neman wa'adin mulki a Aljeriya

Abdoulaye Mamane Amadou
March 7, 2019

Masu zanga-zangar nuna kyama ga tsayawa takarar sake neman wani wa'adi na mulki na iya kai kasar Aljeriya fadawa wani mawuyacin hali inji Shugaba Abdelaziz Bouteflika.

Algerien Algier - Abdelaziz Bouteflika im Rollstuhl zur Wahl 2017
Hoto: Getty Images/AFP/R. Kramdi

Shugaban Aljeriya Abdelaziz Bouteflika ya yi kira ga 'yan kasar da su yi hattara kada su kai kasar ga fadawa a cikin wani yanayi na rashin tabbas.

A wani sakon da shugaban ya aike wa 'yan kasar da aka wallafa a kamfanin dillancin labaran kasar na APS Bouteflika ya yaba wa yadda 'yan kasar suka fito don nuna rashin jin dadinsu a demukradiyyance. To amma kuma ya ja hankali da jama'ar su yi taka tsantsan game da wasu daga ciki ko wajen kasar da ke iya shigowa don bata rawar masu zanga-zangar da tsalle da kuma ke iya kai kasar fadawa cikin wani hali, yana ba da misali da abubuwan da suka faru na yakin basasa a shekarun 1992 zuwa 2002.

Dubun dubatan 'yan Aljeriya ne dai ke ta nuna adawa da bukatar shugaban na tsayawa takara a wani wa'adi na biyar na karagar mulki inda ko a yau wasu lauyoyi suka fito don jaddada wannan matsayi.