1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Aljeriya: Hanyar kawo karshen rikicin Nijar

Abdullahi Tanko Bala
August 29, 2023

A kokarin kawo karshen kiki-kaka na rikicin juyin mulkin soji a Jamhuriyar Nijar, kasar Algeria ta bayar da shawarar wa'adin watanni shida a shirya mayar da kasar kan tafarkin mulkin farar hula.

Niger | Shugaban mulkin sojin Nijar Janar Abdourahmane Tiani
Niger | Shugaban mulkin sojin Nijar Janar Abdourahmane TianiHoto: Balima Boureima/Reuters

Ministan harkokin wajen Aljeriya Ahmed Attaf wanda ya sanar da wannan mataki ya ce gana da kasashen yammacin Afirka kuma dukkaninsu basu amince da matakin da karfin soji wajen kawo karshen rikicin ba.

Shugabannin hafsoshin sojin kasashen ECOWAS dai sun gana a birnin Accra na kasar Ghana domin tattauna yiwuwar tura sojoji Nijar bayan juyin mulkin da dakaru masu tsaron fadar shugaban kasa suka yi a watan yulin da ya wuce.

Kasar ta Aljeriya ta nanata cewa ba ta goyon bayan amfani da karfin soji inda ta yi nuni da sakamakon da ya biyo bayan matakin NATO a Libya a shekarar 2011 lokacin boren juyin juya hali a kan shugaban kasar Muammar Gaddafi.

Aljeriyar ta ce za ta nemi gudanar da taron majalisar Dinkin Duniya domin maido da doka da oda tare da kare hakkin kowane bangare a rikicin da kuma daukar nauyin taron kan halin da ake ciki a yankin Sahel.