1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aljeriya ta koro yan ciranin Afirka 30,000

Gazali Abdou Tasawa
January 15, 2025

Wani sabon rahoto da kungiyar Alarme Phone Sahara da ke sa ido kan `'yan cirani a Nijar ya ce kasar Aljeriya to koro 'yan cirani 'yan Nijar da sauran 'yan kasashen Afirka sama da 30,000 zuwa Nijar a 2024.

Niger Agadez Flüchtlinge
Hoto: BOUREIMA HAMA/AFP

 Wannan na zuwa ne shekara daya baya bayan da hukumomin mulkin sojan Nijar suke soke dokar da ta haramta safarar bakin haure zuwa Turai ta hanyar kasar Nijar, 

Rahoton kungiyar ta Alarme Phone Sahara ya bayyana cewa ‘yan Nijar da ‘yan asalin kasashen Afirka kamar Najeriya, Saliyo, Cote d’Ivoire, Mali, Ghana da dai sauransu da ke kan hanyar zuwa Turai da kasashen Larabawa akalla 31,400 ne hukumomin Aljeriya suka tasa keyarsu zuwa Nijar a 2024 ba tare da lamuncewar mahukuntan Nijar ba. Adadin da kungiyar ta ce shi ne mafi girma na 'yan ci ranin Afirka da Aljeriya ta koro zuwa Nijar a shekarar daya. Dr Chehu Abdoula Aziz shugaban kungiyar ta Alarme Phone Sahara da ta fitar da rahoton ya bayyana halin da 'yan ci ranin da Aljeriya ta koro ke ciki.

'Yan gudun hijira a jihar Agadez, NijarHoto: Jerome Delay/AP/picture alliance


“Idan suka zo cikin kasar Nijar suna cewa a can Aljeriya ana cin zarafinsu, ana gallaza masu, musamman mata da 'yan mata ana yi masu fyade da kwace masu dukiyarsu. To lallai idan sun zo Nijar ba dukansu ne suke samu daukar nauyin kungiyar OIM ba. Wasu na samun kansu a kan titi suna fadawa gidaje neman abinci da sauransu. Kenan annoba ce zuwan nasu"

Shekaru da dama dai kasar Nijar ke korafi kan mataki da Aljeriya ke yin gaban kanta wajen tasa keyar 'yan ci rani na Afirka zuwa Nijar. Lokacin mulkin shugaba Bazoum Mohammed. A watan Aprilun 2024 hukumomin mulkin sojan Nijar sun gayyaci jakadan Aljeriya a Nijar inda suka bayyana masa rashin amincewarsu da matakin da kasar ke dauka. Sai dai kuma Aljeriyar ta ci gaba da aiwatar da matakin lamarin da ya sa Malam Ismael Mohammed na kungiyar Debout Citoyen ya ce ya kamata gwamnatin Nijar ta dauki mataki a kai.

'Yan gudun hijira a jihar Agadez, NijarHoto: Kristin Palitza/dpa/picture alliance

"Kasar Aljeriya ba ta girmama makwabtakar da ke tsakaninmu da ita. Shi ya sa kowane lokaci take zubo mana bakin haure cikin kasa. Kuma a wasu lokuta ba da sanin magabatan Nijar ba. Abu ne da ke ci wa kasa tuwo a kwarya. Amma ya kamata shugaban kasa Abdourahmane Tchiani kar ya yarda ana zuwa ana zube mana mutane kamar shara suna zame mana matsala ya kamata gwamnati ta dauki mataki"

Wannan lamari na wakana ne shekara daya bayan da hukumomin mulkin sojan Nijar suka dauki matakin soke dokar da ta haramta safarar bakin haure da ‘yan ci-rani daga Nijar zuwa Turai da kasashen Larabawa. Malam Tchanga Chalimbo wani dan Nijar dan fafutika ya danganta matsalar da matakin soke wannan doka.

A farkon wannan mako shugaban kasar Nijar Janar Abdourahmane Tchiani ya tsaurara dokokin shigowar baki da ma zamansu a cikin kasar Nijar, dokar da wasu ke ganin za ta iya yin tasiri wajen rage tururuwar ‘yan ci.rani masu hankoran zuwa Turai da kasashen Larabawa.