1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Daukar matakin diflomasiyya a Nijar

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 23, 2023

Ministan harkokin kasashen ketare na Aljeriya Ahmed Attaf ya fara wata ziyara a kasashen yankin Afirka ta Yamma, a wani mataki na lalubo hanyar warware takaddamar makwabciyar kasa Jamhuriyar Nijar.

Aljeriya | Abdelmadjid Tebboune | Nijar
Shugaban kasar Aljeriya Abdelmadjid TebbouneHoto: Sergei Karpukhin/TASS/dpa/picture alliance

A wani rubuto da ya wallafa a ashafinsa na X ko kuma Twitter, ministan harkokin kasashen ketaren na Aljeriya Ahmed Attaf ya nunar da cewa Shugaba Abdelmadjid Tebboune ne ya umurce shi da ya fara ziyara a kasashen Najeriya da Benin da kuma Ghana domin tattauna hanyar diflomasiyya maimakon matakin soja. Aljeriya da ta hada iyakar kimanin kilomita 1000 da Jamhuriyar Nijar dai, na adawa da matakin soja a kan sojojin da suka kifara da gwamnati da kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ke son dauka. Shugaba Tebboune na Aljeriya dai, ya bayyana daukar matakin sojan da barazana ta kai tsaye ga kasarsa.