Alkalan ICC: Gbagbo zai koma gida
January 16, 2019Talla
Kwana guda bayan da Kotun ICC ta yi watsi da gabatar da karar da aka yi a kan Laurent Gbagbo kan laifukan yaki sakamakon rasa rayukan mutane 3000 da aka yi a kasarsa dalilin barkewar rikici bayan zabe.
Alkalan dai sun wanke tsohon shugaban mai shekaru 73 da haihuwa kan laifukan take hakkin bil Adama da ake zarginsa da su. Magoya bayan Gbagbo dai sun taru a gaban kotun ta ICC a birnin na The Hague inda suka shiga tsallan murna yayin da can mahaifarsa mahukuntan birnin Abidjan ko Shugaba Alassane Ouattara, ya ce dawowar sa kasar ba za ta zama barazana ba ga siyasa. Sai dai ba a kai ga sanin ba ko yaushe ne Gbagbo da na hannun damansa Charles Ble Goude za su bar inda ake tsare da su ba karkashin kotun ta ICC.