1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alkalan Nijar na son dawo da kimar shari'a a kasar

Salissou Boukari MAB
July 2, 2021

A Jamhuriyar Nijar, kungiyar alkalai ta SAMAN ta kudiri aniyar dawo da martabar shari’a a kasar, bayan da shugaban kasa Mohamed Bazoum ya nuna aniyar sakar wa shashen shari’a marar gudanar da aiki ba tare da kutse ba.

Revisionsgericht in Niger
Hoto: DW/M. Kanta

Batun tsayar da shari'a ya dade yana ci wa dukannin al'umma tuwo a kwarya a Jamhuriyar Nijar, inda sau tari ake kokawa kan yadda ake gudanar da wasu shari'o'i, ko kuma yadda wasu 'yan kasar suka kasance shafaffu da mai da shari'a ba ta iya kaiwa gare su, musamman wadanda suke kusa da masu mulki. Sai dai a daya hannun ake neman inda wanda ke adawa ya yi laifi domin a gurfanar da shi a gaban kuliya. Amma da alama wannan matsala ta kusa zama tarihi idan aka yi la'akari da matakin da kungiyar alkalai ta kasar Nijar take shirin dauka domin maido da martabar shari'a a.

Tuni dai wannan yunkuri na samar da shari'a ta gaskiya a kasar Nijar ya dauki hankalin kungiyoyin fararen hula da 'yan siyasa. A cewar Bana Ibrahim mai fafutika a yanar gizo, shekaru 10 da suka gabata shari'a ta taka mummunar rawa kan abubuwa da dama a Nijar. Ko shi ma Alhaji Doudou Rahama, dan siyasa da ke bangaren adawa, wanda a kullum yake fafutikar ganin an kamanta gaskiya a fannin na shari'a, ya yaba wannan yunkuri.

Zaben 2021 ya fitar da rarrabuwar kawuna kan fannin shari'a a Nijar

Sau tari 'yan fararen hula sun fuskanci matsaloli saboda yadda suke nuna adawa da wasu manufofi na gwamnatin da ta shude, inda wasu ke zargin ta da amfani da shari'a wajen garkame wasu da ake ganin suna hana ruwa gudu. A cewar Alhaji Idi Abdou dan kungiyar farar hula da ke kare hakkin jama'a, a halin yanzu kallo ya koma ga alkallan kasar ta Nijar kan yadda za su gamsar da 'yan kasa da ma duniya a nan gaba:

An zura ido a gani ko lamarin zai zama fada da cikawa daga bangaren shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum, wanda ya nuna kyaukkyawar aniya ta sakar wa sashen shari'a mara domin ya yi aikinsa ba tare da wani kutse daga gwamnati ba. Sannan su kansu alkalan za su kiyaye duk wata maja-maja da ake zargin su da aikatawa idan ana shari'a tsakanin wani hamshakin mai kudi da talaka.?