Alkiblar da Putin ya dauka ta ba shi nasara a zabe
March 19, 2018Shugaba Vladimir Putin ya sake samun nasara a zaben shugaban kasar Rasha da aka yi a ranar Lahadi, abin da ke sake ba shi damar sake jan ragamar kasar tsawon shekaru shida, lamarin da ke zuwa a daidai lokacin da mahukuntan na birnin Moscow ke kara samun tsamin dangantaka da kasashen yamma.
Shugaba Putin da ya mulki Rasha kusan tsawon shekaru 20 ya samu rinjaye gagrumi na sama da kashi 70 cikin dari, sakamakon da ke zama mafi kyau ga Putin da 'yan adawa ke bayyana shi a matsayin sakamakon rainin hankali.
Masu sanya idanu dai sun bayyana zargin magudi a zaben da mahukuntan na fadar Kremlin suka yi kokari na ganin ya ba wa Putin dama ta ci gaba da jan ragamar kasar a karo na hudu da zai kafa tarihi. Putin dai ya kara da 'yan takara bakwai ciki kuwa har da babban dan adawa Alexei Navalny da aka haramtawa shiga harkokin na zabe saboda wasu dalilai na shari'a. Lamarin da ya sa sakamakon zaben bai zamo da mamaki ba kamar yadda Valentina Belyatskaya wata 'yar kasar ke cewa:
"Na yi amannar cewa shi ne kadai zai iya ci gaba da samar da daidaito a wannan kasa."