Allah Ya yiwa shugaban Kosovo Ibrahim Rugova rasuwa
January 21, 2006Shugaban lardin Kosovo Ibrahim Rugova wanda yayi fama da cutar kansa ta huhu ya rasu a yau asabar, inji jami´an Kosovo dake kurkusa da shugaban dan shekaru 62 a duniya. Wani jami´in yamma a Pristina babban birnin Kosovo ya tabbatar da rasuwar shugaba Rugova. To sai dai ya ce ka da a ambaci sunansa domin ba´a ba shi izinin ba da wannan sanarwa a bainar jama´a ba. Ibrahim Rugova wanda ke jagorantar gwagwarmayar kwatar ´yanci ´yan kabilar Albaniya daga Sabiya, a cikin watan satumban bara a hukumance aka tabbatar da kamuwarsa da cutar kansa ta huhu. Shugaba wanda ke da farin jini a tsakanin Albaniyawa ya kasance mai yawan shan taba sigari har zuwa lokacin da aka tabbatar da cutar a jikinsa. Rasuwarsa dai ta zo a wani lokaci mai daure kai ga Kosovo, wadda ke shirin fara tattaunawa ko ta karbi ´yanci ko kuma ta ci-gaba da zama karkashin yankin Sabiya.