1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Almajiran Zakzaky sun kai ziyara ga Dahiru Bauchi

June 8, 2018

Almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky sun kai ziyarar sada zumunci na azumin watan Ramadan ga Sheikh Dahiru Usman Bauchi kan mahimancin kyautata zamantakewa.

Nigeria Demo für die Freilassung von Ibraheem Zakzaky
Hoton wasu mabiya Ibraheem Zakzaky lokacin wani gangamiHoto: picture alliance/AP Photo/M. Giginyu

 

Wannan tawaga dai ta daukacin almajirai da shehunan malaman Shia  da ke a karkashin kungiyar Islamic Movement of Nigeria ta  Sheikh Ibraheem Zakzaky, an shirya ta ne domin dai kara kullun dankwan zumunci da fahimtar juna tsakanin kungiyoyin Musulman Najeriya tare da kuma yin anfani da lokacin azumin wajen kara bullo da hanyoyin mutunta manyan malamai ta hanyar kai masu ziyara bangajiya

Mallam Aliyu Turmizi  shi ne dai wanda ya  jagoranta zuwa kai ziyarar ganawa ta azumin watan Ramadan zuwa ga Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya kuma yi masa godiya ga yunkurin da yake yi na neman hada kan Musulma.

Su kowa dai har kullun kungiyoyin kare ‘yancin bil Adam kira ne suke yi  a kan bukatar bayar da belin Ibraheem Zakzaky da kuma janyo hankalin gwamnatin tarayyar Najeriya a kan bin umarnin hukuncin da babban kotun Abuja ta yank.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani