1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alpha Condè ya lashe zabe

October 24, 2020

An bayyana shugaban kasar Guinea mai ci a matsayin wanda ya lashe zaben da ke cike da rudani gami da fitintinun bayan zabe. Wannan dai zabe ne da hankali ke kansa.

Guinea Alpha Conde
Hoto: Facebook/Alpha Condé

Hukumar zabe a kasar Guinea Conakry, ta bayyana Shugaba Alpha Conde, a matsayin wanda ya lashe zaben kasar inda ya sami kashi 59% na kuri'ub da aka kada a makon jiya.

Hukumar zaben ta Guinea ta kuma ce babban abokin hamayyar Shugaba Conde, Cellou Dalein Diallo, ya samu kashi 33.5% na kuri'un, mutumin da da dama ya bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben.

Yanzu dai Shugaba Alpha Condè zai zama shugaban da zai mukli Guinea har sau uku, bayan sauya tsarin mulki da aka yi wanda ya ba shi damar takara.

Sabbin rikice-rikice dai sun sake barkewa a Guinea ranar Juma'a, a tsakanin dakarun gwamnati da magoya bayan babban abokin hamayyar Shugaba Alpha Cònde, wato Cellou Dalein Diallo, yayin da ake dakon sakamakon zaben da ak yi a karshen makon jiya.

Rahotanni daga kasar a yanzu na cewa ana zaman dar-dar bayan sanar da sakamakon da hukumar zabe ta yi.

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW