Alqaida na kara fadada ayyukan ta a duniya inji Amurka
January 12, 2007Shugaban hukumar leken asiri ta Amurka, Mr John Negroponte yace, wasu shugabannin kungiyyar, Alqaida sun samu mafaka a kasar Pakistan.
Mr Negroponte, yaci gaba da cewa wannan sabuwar mafaka da jami´an kungiyyar ta Alqaida suka samu, ya basu damar kara daura damara a ayyukan su na ta´addanci.
A cewar babban daraktan , jami´an kungiyyar ta Alqaida a yanzu na samun ci gaban yaduwar kungiyyar su , a yankin gabas ta tsakiya da arewacin Afirka da kuma nahiyar turai.
Kusan a yanzu a cewar Mr Negroponte, kungiyyar ta Alqaida, kungiyyace, data kasance mafi girma dakewa duniya barazana. Barazana.
Idan dai an iya tunawa, a farko farkon wannan makon da muke ciki ne dakarun Amurka suka kaddamar da wani hari a somalia, da nufin halaka yan kungiyyar ta Alqaida ,da ake tunanin na da mafaka a kasar.