1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zabe ya gudana cikin tsanaki a Nijar

Salissou Boukari LMJ
December 28, 2020

A Jamhuriyar Nijar har yanzu ana ci gaba da dakon sakamakon zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki da ya gudana a karshen mako a fadin kasar.

Niger Wahlzentrale Niamey
Ofishin Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Kasa CENI, a Jamhuriyar NijarHoto: DW/A. Adamou

Ga yadda aka saba dai tun cikin daren da aka kammala kada kuri'a, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa CENI ke soma bayar da sakamako, musamman ma na zaben shugaban kasa. Sai dai za a iya cewa ganin yadda 'yan takara suka yi yawa a daidai wannan lokaci, inda ake da sunayen 'yan takara kimanin 30 a takardar zaben. Koda yake biyu daga cikinsu sun janye, amma ana ganin hakan ne ya kawo tsaiko wajen tattara sakamakon zaben tun daga mataki na runfuna zuwa cibiyar hukumar zabe ta kananan hukumomi, kafin hukumar zabe ta jiha ta tantance kana ya isa shalkwatar hukumar zabe ta kasa, wadda ke da ikon bayar da sakamakon.

Karin Bayani: HALCIA za ta kasa ta tsare a zaben Nijar

Daga bangaren masu sanya idanu na cikin gida kamar kungiyar OPELE da suka aike da wakilansu kimanin 500 a fadin kasar ta Nijar, sun ce zaben ya gudana cikin tsanaki, sai dai kuma akwai kura-kurai da ya kamata a gyara da kuma bayar da sakamakon da ya fito daga runfunan zabe ba tare da an canza ba. 

Daga bangaran jam'iyyun siyasa da suma suka yi nasu sa idanun kan yadda zaben ya gudana a fadin kasar, a cewar Bana Ibrahim na jam'iyyar Lumana Afrika ta hama Amadou da ta bayar da goyon baya ga dan takarar jam'iyyar RDR Canji Alhaji Mahamane Ousmane, suna da kwarin gwiwa sosai dangane da sakamakon da suke samu daga sassa daban-daban na Jamhuriyar ta Nijar. 

Karin Bayani: Zargin magudi a zaben kananan hukumomin Nijar

Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa kan batun zaben, Hafizou Malam Bachir da ke zaman mai magana da yawun jam'iyya mai mulki ta PNDS Tarayyar a jihar Damagaram, ya ce sun gamsu da yadda ya gudana har ma ya isar da godiya ga dukkanin jam'iyyun da suka shiga aka fafata da su har ma 'yan adawa, bisa yadda aka yi zaben cikin kwanciyar hankali.

Karin Bayani: Zaben Jamhuriyar Nijar cikin tsanaki

Zaben Jamhuriyar Nijar

03:08

This browser does not support the video element.

Suma kungiyoyin kasa da kasa kamar kungiyar Kasashen Yankin Sahel da sahara ta CEN SAD da ta yi aikin sanya idanu a zaben na Nijar, ta ce abubuwan da ta gani ya nunar da cewa an kada kuri'u cikin tsanaki da kwanciyar hankali. Koda yake ta nunar da cewa akwai wasu 'yan kananan kura-kurai da suka hadar da lattin kai kayan zabe a wasu wuraren. Sai dai kuma za a iya cewa wannan zabe da alama zai sha bam-bam da wadanda aka yi a 'yan shekarun da suka gabata, inda kowanne bangare ke kan bakansa na cewa ba zai taba yarda a karkatar kuri'un da aka rigaya aka kidaya ba, wato na sakamakon da ya fito daga runfunan zabe saboda wata manufa ta daban ba.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani