1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaUkraine

Ana jimamin mutuwar dumbin mutane a Ukraine

Abdoulaye Mamane Amadou
October 6, 2023

Shugaba Volodymyr Zelensky ya bayyana harin da ya kashe mutane 51 da dakarun Rasha suka kai a gabashin Ukraine a matsayin na rashin imani

Themenpaket | Ukraine Drohnenangriff auf Kharkiv
Wasu daga cikin gawarwakin mutanen da harin ya rutsa da suHoto: REUTERS

Ukraine na cigaba da jimamin mutuwar 'yan kasarta 51 da suka cika sakamakon luguden wutar da dakarun Rasha suka yi a kauyen Groza da ke yankin Kharkiv a gabashin kasar.

Karin Bayani:  Ukraine za ta samu karin tallafi daga Jamus

Jami'an agaji sun ce ko baya ga mutanen 51 da suka mutu ciki har da wani yaro karami, akwai akalla mutane shida da suka ji mummunan rauni biyo bayan luguden wutar da Rasha ta kai ana tsaka da jana'izar wani soja.

Shugaba Volodymyr Zelensky da ke halartar wani taron koli na jagororin nahiyar Turai ya yi Allah wadai da harin, yana mai bayyana shi a matsayin na rashin imani, kana ya bukaci karin tallafin Turai wajen kare 'yan kasar.

Karin Bayani:  Taron kawayen Ukraine

Tuni ma dai kasashen nahiyar da dama suka soki harin, Jamus ta kara jaddada matsayinta na cigaba da taimakawa Ukraine, gwamnatin Berlin ta ce za ta ba wa Ukraine tallafin makamai a wani mataki na kare 'yan kasar daga ruwan bama-baman Rasha.