1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'umma na jiran sakamakon zabe a Liberia

Abdullahi Tanko Bala
October 10, 2017

'Yan Liberia sun kada kuri'ar zaben wanda zai gaji shugabar kasar mai barin gado Ellen Johnson Sirleaf wadda ta shafe shekaru 12 tana jan ragamar mulkin kasar.

Liberia Monrovia Wahlen
'Yan Liberia sun gudanar da zabukan kasaHoto: Reuters/T. Gouegnon

Dubban jama'a ne dai suka yi dafifi akan layi a rumfunan zabe cike da farin ciki domin kada kuri'iunsu. Tun da karfe 8:00 na safe aka bude rumfunan zaben wanda ake fatan mika mulki cikin ruwan sanyi da lumana a karon farko cikin shekaru 73 daga shugabar kasar mai barin gado Ellen Johnson Sirleaf wadda ta sami lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel da kuma ake yiwa kirari da mace mai kamar maza kwari ne babu, bayan wa'adin mulki na shekaru shida sau biyu da ta yi tana mulki.

Makomar Liberia a hannun 'yan kasa masu zabe

Shugaba mai barin gado Ellen Johnson Sirleaf ta yi zabeHoto: dapd

Mutane miliyan biyu da dubu dari daya da suka yi rajista ke kada kuri'ar a rumfunan zabe 5,400 a fadin kasar. Galibin yan kasar dai musamman matasa da ke kada kuri'arsu a karon farko na fatan gudanar da zaben lami lafiya. Manazarta al'amuran siyasa dai na cewa daga cikin yan takarar 20 da ke neman shugabancin kasar, yan takara uku ne ake gani suke iya samun nasarar lashe zaben. wadannan kuwa sun hada da mataimakin shugaban kasar Joseph Boakai na jam'iyya mai mulki ta Unity Party da tsohon zakaran kwallon kafa na duniya George Weah da ke jagorantar kawancen jam'iyyun adawa na CDC sai kuma Charles Brumskine na jam'iyyar Liberty.

Bisa ga yawan yan takarar da ke neman shugaban kasar dai, zai yi wuya ga dan takara daya ya iya samun kashi 50 cikin dari na kuri'un, wanda hakan ke nufin cewa sai an je kenan ga zagaye na biyu mai yiwuwa a cikin watan Nuwamba. Masu sa ido na cikin gida da na sauran kasashen duniya da kungiyar Tarayyar Turai dana kungiyar Tarayyar Afirka da kuma ECOWAS da ma cibiyoyin nazarin dimokradiyya sun zagaya sassa daban-daban na kasar domin ganin yadda zaben ya gudana.

Zaben na zaman zakaran gwajin dafi ga Liberia

Maluman zabe a runfar zabe a LiberiaHoto: dapd

Kawo yanzu babu rahoton wata tarzoma ko tashin hankali da aka samu. Wakilin sakataren Majalisar Dinkin Duniya kuma shugaban tawagar wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Liberia Farid Zarif ya yaba wa 'yan Liberia yadda suka gudanar da yakin neman zabe lafiya da kuma zaben da ya gudana cikin kwanciyar hankali. Dukkan dai wanda ya yi nasarar maye gurbin Shugaba Ellen Johnson Sirleaf ya na da babban kalubale a gabansa, a kasar da ke fama da talauci sannan kashi 85 cikin dari na matasa basu aikin yi.