1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Kokarin sabunta katin zabe

Muhammad Bello LMJ
June 14, 2022

Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Kasa a Najeriya INEC, ta ce sha'awar 'yan kasar ta sabunta katinsu na zabe wato PVC ta karu sosai a baya-bayan nan.

Najeriya I Zabe I Katin Zabe
Wadanda ke da katin zabe ne kadai, za su samu damar kada kuri'a a zaben NajeriyaHoto: DW/K. Gänsler

A cewa Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Kasar a Najeriya wato INEC, cincirundon 'yan kasar da ke kokarin sabunta katunan nasu na zeb ya sake haifar da babban kalubale na iya sabunta katunan ga masu bukata. Hukumar ta INEC tace, tafi fuskantar cunkoson masu neman sabunta katinan nasu ne a yankin Igbo da ke da jihohi biyar da kuma jihohin Lagos da Kano. A cewar hukumar a baya dai ba ta samun irin wannan cunkoso gabanin zabe, tana mai cewa ya zame mata dole ta kara tura kayayyakin aiki zuwa jihohin kasar domin tunkarar kalubalen da take fuskanta ta cuncirundon mutanen gadan-gadan cikin wa'adin kwanakin da ta kayyade. Ana dai iya cewa al'ummar kasar ta fara fahimtar muhimmancin katin zaben, sakamakon wayar da kan da kungiyoyi masu zaman kansu musamman ma na matasa ke yi.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani