1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Zanga-zangar tsadar rayuwa a Benin

May 12, 2024

Dubban al'umma sun fantsama kan titunan birnin Cotonou cibiyar kasuwancin Jamhuriyar Benin domin kalubalantar tsadar rayuwa da kuma take-taken hakkin dan Adam da 'yancin 'yan kwadago.

Benin | Demonstration gegen hohe Lebenserhaltungskosten in Cotonou
Hoto: Abadjaye Justin Sodogandji/AFP/Getty Images

Masu zanga-zangar da manyan kungiyoyin kwadago na Benin suka kira a ranar Asabar, sun kewaye manyan titunan birnin Cotonou cibiyar kasuwancin kasar tare da rakkiyar 'yan sanda, suna furta kalamen cewa 'sun gaji da halin matsi da kuma yunwa.'

Karin bayani: 'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a Benin

Masu aiko da rahotanni sun ambato babban sakataren kungiyar kwadago ta Benin Anselme Amoussou na cewa: 'Lokaci ya yi da za a zage dantse domin samar da gwamnati mai sassauci, sannan kuma daga wannan lokaci sun daina barin mutun guda ya yanke shawara kan makomar kasa baki daya.'

Karin bayani: Rikici tsakanin Nijar da Jamhuriyar Benin

Yau da 'yan watanni kenan da farashin kayyaki ya yi tashin gauron zabi a Benin tun bayan rufe iyakokin kasar da makwabciyarta Nijar da ta fuskanci juyin mulki a watan Yulin bara.

Baya ga haka ma janye tallafin man fetur da gwamnatin Najeriya ta yi a lokacin zuwan shugaba Bola Tinubu kan gadon mulki ya taka rawa wajen jefa al'ummar Benin cikin wannan yanayi.