Al'ummar Burkina Faso na gudanar da zanga-zanga
July 3, 2021Mika bukatar hakan da kakkausar murya, na zuwa ne bayan da wasu 'yan bindiga suka halaka kimanin mutane 130 a watan da ya gabata.
Masu zanga-zangar a birnin na furta kalamai da cewa, a tsaurara matakan tsaro tare da sanya ayar tambaya ko akwai wanda ke shugabancin kasar. Wannan dai shi ne karo na farko da bangaren adawar kasar da sauran kungiyoyin fararen hula suka shirya zanga-zanga, tun bayan sake zaben Shugaba Roch Marc Christian Kabore a bara.
A cewar madugun adawar kasar Eddie Komboigo Burkina Faso ta fuskanci mummunan zubar da jini tun a wa'adin mulkin shugaban na farko, a don haka suke fargabar abin da ka iya biyo baya a yanzu. To sai dai a martanin shugaban kasar tun bayan cece-kucen da ya barke a kasar daga watan Yuni, a ranar Larabar da ta gabata ya tsige ministan tsaronsa, inda yake rike da mukamin a yanzu.
Tun daga shekarar 2015 dai, kasar Burkina Faso da ke yankin yammacin Afirka ke fama da hare-haren mayakan Al-Qaeda da kuma IS.