1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasuwar shugaba Deby ta girgiza Chadi

Abdullahi Tanko Bala
April 22, 2021

A ranar talata 20 ga watan Afrilu sojojin Chadi suka bada sanarwar Allah ya yi wa shugaban kasar Idriss Deby Itno rasuwa a fagen Daga yayin da yake bada umarni ga sojojin kasar da ke yaki da 'yan tawaye.

Todesfall Präsident des Tschad Idriss Deby gestorben
Hoto: Regis Duvignau/AP/picture alliance

Mutuwar shugaba Idriss Deby wanda ya shafe fiye da shekaru 30 a karagar mulki ta jefa al’umma musamman a N’Djamena babban birnin kasar cikin rudani da rashin tabbas game da makomar kasar. Tuni sojojin suka nada dan Idriss Deby Mahamat domin maye gurbin mahaifinsa.

Karin Bayani:  Ana samun sabanin fahimta kan makomar mulkin Chadi

Hoto: Marco Longari/AFP/Getty Images

Sojojin dai sun jingine kundin tsarin mulki sannan an rushe gwamnati yayin da suka kafa majalisar soji ta wucin gadi wadda za ta jagoranci kasar.

Kasar Chadi ta dade tana fama da rikicin tawaye. Sai dai a baya bayan nan 'yan tawayen wadanda suka yi sansani a kasar Libya sun kudiri aniyar ganin bayan Deby  inda suka kaddamar da hare hare domin shiga N'Djamena babban birnin Chadi kamar yadda suka yi ikrari.

Majalisar soji ta wucin gadi karkashin jagorancin Mahamat Debyta yi alkawarin mayar da kasar kan turbar dimukuradiyya nan da watanni 18. Sai dai ‘yan adawa sun soki lamarin wannan mataki da suka baiyana da cewa tamkar juyin mulki ne.

Shugabannin kasashe da suka hada da Faransa wadda ta yi wa Chadi mulkin mallaka sun baiyana shugaban da ya rasu Idriss Deby a matsayin jan gwarzo yayin da suka bukaci dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

     

Tsallake zuwa bangare na gaba Rahotanni da Sharhuna