1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ghana: Ana dakon sakamakon zabe

December 8, 2020

A yayin da Hukumar zabe EC ke baiyana sakamakon zabe na kananan mazabu, dan takaran jam'iyya NDC mai Mulki kuma mai neman yin tazarce, Shugaba Nana Akufo-Addo na ikirarin cewa shi ne kan gaba a zaben.

Ghana Wahlen Abstimmung Auszaehlung Warten
Hoto: AP

Huukumar zaben Ghana ta shaida cewar za ta sanar da sakamakon zabukan a cikin sa’o’I 24 bayan da aka kamalla gudanar da zabukan, inda ta bayyana cewar ta tsawala dukkanin matakai tare da bai wa jami’anta horon tabbatar da zaman lafiya. Sai dai kawo yanzu babu wani takaimemen bayani daga hukumar bayan sa’o’I 19 da kamala kada kuri’u a kasar. Shi kuwa Shugaban kasar Nana Akuffo Addo na ikirarin lashe zaben. Karin bayani: Ana ci gaba da tattara sakamakon zaben Ghana

Yan takara 12 ne suka fafata a babban zabenHoto: Reuters/L. Gnago

Kawo yanzu Hukumar zaben Ghana EC ba ta ce komai a game da wani sakamakon zabe, inda a duk kokarin jiyo ta bangaren hukumar hakar wakiliyarmu a Accra bata cimma ruwa ba, domin babu wanda ke amsa wayar da tayi ta bugawa. Hakazalika a dangane da wannan batu ne ma Jam’iyyar NDC wacce takarar tafi tsananta a tsakanin ta da jam’iyyar NPP mai mulkin kasar, ta ce babu yadda za’a yi hukumar zabe ta iya bayyana sakamakon a cikin sa’o’I 24, inda sakamakon wanan ikirarrin ma ta gudanar da wani taron manema labarai da sanyin safiyar wannan Talata. Karin bayani:Ghana: Yarjejeniyar zaman lafiya kafin zabe

Sama da mutane miliyan goma sha bakwai ne suka kada kuri'unsu a zaben a yayin da 'yan takara goma sha biyu suka tsaya takarar neman shugabancin kasar a zaben da aka gudanar a ranar Litinin da ta gabata. Sai dai hankula sun raja'a a kan manyan jam'iyyun NPP na Shugaba Nana Akufo Addo da kuma jam'iyyar NDC ta tsohon Shugaban kasar John Dramani Mahama. Kowane dan takarar dai na fatan samun kaso 50 na kuri'un ko kuma a je zagaye na biyu. Gyara tattalin arziki da aikin yi su ne kan gaba cikin kalubalen da ke jiran duk wanda ya yi nasara a zaben.

Akwai kuma 'yan takara 918 da ke neman kujerun majalisar dokokin Ghanan 275. Rahotanni dai na cewa zaben na gudana cikin kwanciyar hankali ba tare da matsala ba, yayin hukumar zabe ta yi alkawin sanar da sakamakon zaben ba tare da jinkiri ba dazarar komai ya kammala.