An fara zaben shugaban kasa a Guinea
December 28, 2025
'Yan takara guda tara ne ke fafatawa a zaben ciki har da shugaban gwamnatin mulkin sojin kasar Janar Mamadi Doumbouya mai shekaru 41, wanda ya yi amai ya lashe game da tsayawarsa takara kuma hasashe ke nuna cewa zai lashe zaben wanda aka haramta wa manyan 'yan adawa tsayawa takara.
Kimanin masu kada kuri'a miliyan 6.8 ne ake sa ran za su fita runfunan zaben da aka bude da kimanin karfe bakwai na wannan safiya kuma za a rufe su da kimanin karfe shida na maraicen yau.
Masu aiko da rahotonni sun ce zaben na gudana cikin tsauraran matakan tsaro, sai dai jiya Asabar jami'an tsaron kasar sun ce sun dakile 'yan wata kungiya masu dauke da makamai da ke barazanar yin zagon kasa ga tsaron kasar a unguwannin marasa galihu na birnin Conakry.
Sai dai a ranar Juma'a da ta gabata MDD ta yi Allah wadai da yanayin da aka gudanar da yakin neman zaben na Guinea musamman ma barazana da ta ce an rinka yi wa 'yan adawa.